Acts 28

Tsibirin Malta

1Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne. 2Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi. 3Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya ɗafe a hannunsa. 4Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.” 5Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba. 6Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke raʼayi suka ce shi wani allah ne.

7Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku. 8Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yǎ gan shi, bayan ya yi masa adduʼa, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. 9Saʼad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su. 10Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata.

Isowa a Roma

11Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci dammuna a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus. 12Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku. 13Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Washegari iskar kudu ta taso, washegari kuma muka kai Futeyoli. 14A can muka tarar da waɗansu ʼyanʼuwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma. 15ʼYanʼuwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa. 16Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yǎ zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa.

Bulus Ya Yi Waʼazi a Roma a Tsare

17Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu: “ʼYanʼuwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da alʼadun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. 18Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. 19Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar-ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba. 20Saboda wannan ne na nemi in ganku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Israʼila ne, nake a ɗaure da wannan sarƙa.”

21Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ʼyanʼuwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai. 22Amma muna so mu ji raʼayinka, gama mun san cewa mutane koʼina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.”

23Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yi musu bayyani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa. 24Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba. 25Suka kāsa yarda da juna suka fara watsewa bayan Bulus ya yi wannan magana guda cewa: “Ruhu Mai Tsarki ya faɗa wa kakannin-kakanninku gaskiya saʼad da ya ce ta bakin annabi Ishaya cewa:

26“ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce,
“Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba;
za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”
27Gama zuciyar mutanen nan ta yi tauri;
da ƙyar suke ji da kunnuwansu,
sun kuma rufe idanunsu.
In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,
su ji da kunnuwansu,
su fahimta a zukatansu,
su kuma juyo, in kuwa warkar da su.’
Ish 6.9, 10

28“Saboda haka na so ku san cewa an aika da ceton Allah ga Alʼummai, za su kuwa saurara!”
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da saurara!” 29 Bayan ya faɗi haka, sai Yahudawa suka watse, suna gardama sosai a junansu.


29
This verse is empty in this translation.
30Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana maraba da duk wanda ya je wurinsa. 31Gabagaɗi ba tare da wani hani ba, ya yi waʼazin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi.

Copyright information for HauSRK